Daga:
Maje El-Hajeej Hotoro
Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC ta kasa sun nemi a yi zaben K'ato bayan K'ato wajen fitar da 'yan takara daga Shugaban Kasa zuwa Gwamna har 'yan majalisar jihohi. Amma garda-gar Gwamnoni suka bijire suka ce ba su yarda ba.
Saboda idan aka ba wa TALAKA wannan damar zai zabi wanda ya ke so ya kuma kayar da wanda ba ya so. Idan aka yi haka Gwamnoni sun rasa damar kawo wanda suka ga dama su hana wanda suka ga dama tikitin takara.
A lalacewar siyasar mu, wasu tsirarun mutane da ake kira WAKILAI (delegate) wanda jam'iyya take nadawa bisa son zuciya sune ake ba wa damar zabawa Miliyoyin Talakawa 'yan takara. Su kuma wadannan wakilai zama ake yi da su a yi ciniki nawa zan bayar ku zabe ni, wanda ya fi lafta kudi su zabe shi.
Sannan shi kuma ya karya hula ya nufo Talakawa yana bugun kirjin "Ni Masoyin Buhari Ne Akan Buhari Sai Dai A Mutu". Gwamnoni nawa ne suke bugun kirjin su Masoya Buhari ne? Shin tunda Buhari ya zama Shugaban Kasa akwai Gwamnan da ya taba rikewa kudin jiharsa da dokar kasa ta amince a ba shi ya hana shi? Tsakani da Allah Gwamnoni Nawa ne suke ba wa kananan hukumomin jiharsu kudinsu kai da kai kamar yadda Buhari yake ba su?
Kiri-kiri kana ganin Gwamnoni na shan jinin TALAKA amma kana sukar su sai su fake da Buhari suna kiran ka da wai kai Makiyin Buhari ne. Shin don kana Jam'iyyar APC shikenan ka zama Buhari? Idan da gaske Ku masoya Buhari ne ya yarda ya amince a yi zabensa K'ato bayan K'ato kai me ya sa ba za ka yi koyi da shi ba?
Me ya sa ko Gwamna daya ba zai bugi kirji ya kalli Talakawa ya ce "A matsayina na mai akidar Buhari mai son a kawo sauyi a Najeriya, na amince Talakawa su yi amfani da nagarta ta, da kuma ayyukan alheri na su yi zaben K'ato bayan K'ato, Hajiya bayan Hajiya su zabe ni kamar yadda za a yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari".
Amma an bar jam'iyya a hannun 'yan siyasa suna nada yaransu a matsayin wakilai su zare musu ido ga wanda muke so ka zaba idan ka ki a cire ka a sa wani. Dan takara ya zauna da su ya ba su manyan kudade, sannan ya bi wakilai ya sayi takarar sa. Su kuma su zabe shi su kawar da kansu ga duk wani mai mutunci da nagarta matukar ba zai biya su ba.
Ba ruwansu da lalacewar sa, ba ruwansu da bakin halinsa ba kuma ruwansu da munanan Dabi'unka. Kai ko da fasikancinka ya bayyana k'arara, idan ka ce wane fa da kuka zaba mana tantirin Dan Giya ne, Dan Luwadi ne, shahararren mazinaci ne, za su ina ruwanmu kudi ya biya mu. Ko kuma umarni aka ba mu.
Shin wannan Ita ce siyasar da ake yi wa kirari da "Gwamnatin TALAKA daga TALAKA zuwa ga TALAKA?
A ranar zaben fidda gwani Tsakanin Buhari, Kwankwaso da Atiku, fadawa Wakilai yayi k'ek'e da k'ek'e ba ni da Dala ko Naira da zan ba ku, amma idan na zama Shugaban Kasa zan ba da rayuwata ga Najeriya.
BA WANI GWAMNA DA ZAI IYA KWATANTA WANNAN?
Post a Comment
Post a Comment