
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi watsi da jar hula a yayin da tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ya kai masa ziyara ranar Asabar, jim kadan bayan ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Sanya jar hula alama ce ta yin biyayya ga sanata Rabi'u Kwankwaso, mutumin da suka raba gari da Gwamna Ganduje bayan sun yi shekara da shekaru suna harokokin siyasa tare.
Malam Shekarau, wanda ya ziyarci Gwamna Ganduje sanye da bakaken tufafi, ya taras da Gwamna Ganduje sanye da nasa bakaken tufafin, ciki har da bakar hula - ba ja ba - kamar yadda ya saba.
Madafa: BCC
ku rubuta mana ra'ayoyinku ta hanyar comment, don yanada matukar amfani..
Post a Comment
Post a Comment