Wani yaro dan shekara biyu mai suna Rapi Ananda Pamungkas a garin Sukabumi na kasar Indonesiya ya zama abin al’ajabi saboda yadda yake shanye karan taba 40 a kullum.
Rapi Ananda Pamungkas, ya fara shan taba ce daga tsintar wasu abubuwan da suke kama da karan taba da aka watsar a shagon mahaifiyarsa, sai wadansu yara da suka girme shi suka fara kunna wa abin da ke kama da tabar wuta.
Bayan zukar abu mai kama da taba, ba a dade ba sai ya fara bin shaguna da nufin su ba shi tabar.
Masu sayar da tabar na ganin yaron a matsayin mai karancin shekaru da ke da irin wannan hali na shan taba, sun yi mamakin yadda da zarar sun mika wa Rapi Ananda Pamungkas taba sai ya kunna mata wuta kamar yadda ake yi ya kama zuka.
A lokacin da Rapi ke zukar tabarsa zaune a kan wani babur jama’a masu wucewa na kallonsa a matsayin yaro mai karancin shekaru amma mai dabi’ar manya.
A lokacin da masu wucewar ke kallon Rapi na zukar tabarsa, wadansu kan yunkura don karbe tabar amma sai ya bata rai kamar ana so a rage masa jin dadi. Shi dai Rapi a duk lokacin da yake shan tabarsa bai damuwa da masu kallonsa, kawai yanayin abin da yake so ne.
Mahaifiyar Rapi, Maryati mai shekara 35, ta ce, tana saya wa danta kwalin taba biyu kullum don guje masa shiga mummunan hali.
Maryati ta ce, dan nata na jin dadin zukar taba ce duk lokacin da yake shan kofi da cin kek. Rapi dai na shan taba kullum kimanin wata biyu da suka gabata, kuma duk lokacin da bai samu taba ba yana fita cikin hayyacinsa.
Maryati ta ce, abu ne mai wahala ta dakatar da danta daga shan tabar, saboda duk lokacin da bai sha ba, wuni zai yi yana kuka, yayin da kuma bai iya barci idan bai sha ba sai ya yi ta rusa kuka kawai.
Mahaifin Rapi, Misbahudin mai shekara 40 wanda shi ma yana shan taba ya ce, ya yi mamakin yadda dansu ba ya jin dadin rayuwarsa idan bai sha taba sigari ba.
Post a Comment
Post a Comment