Shugaba Muhammadu Buhari ya Sanya farin ciki da annushuwa a fuskokin wasu yan kasuwa akalla dubu ashirin da bakwai 27000 dake Jihar Oyo da tallafin kudaden kasuwanci na Trader Moni a turance.

Anan wasu yan kasuwa ne a kasuwar  Bola Ige Gbagi dake Ibadan a jahar Oyo suke rawa da shewar a lokacinda suka karbi tallafin bashi maras ruwa na naira dubu goma (N10,000) domin Sana'a a Yayinda mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin a Ibadan

Koda yake yan adawa sunata ihun wai kudin yayi Kadan amma ga jama'ah yan kasuwa nata murna da samun tallafin inda sukace babu wata gwaunatin data taba tunawa dasu tayi musu hakan.

Haka kuma sun kara da Cewar Baba Buhari ya zarce 2019 domin Idan bai zarce ba suna cikin damuwa

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.
Sai Baba 2019


 
Top