Jami’an ‘yan sanda a garin Kalaba ta jihar Kuros Riba sun bada sanarwar cafke wasu mata da miji da suka bada dansu mai shekara biyu a matsayin jingina sun karbar bashin Naira 180,000 daga wata mata mai safarar mutane. 

Mutumin mai suna Daniel Bassey ya ce ba siyar da dan nashi ya yi ba, ya dai bayar da shi ne a matsayin jingina saboda ya samu ya biya kudin hayar gidan da yake zama, saboda a cewar shi da damina babu wani aiki da yake samu ya yi balle ya samu kudin shiga. 

‘Abokina ne ya bani shawarar bada dan nawa a matsayin jingina, ta yadda in na samu kudin daga baya zan je in karbi dana, sam-sam ba siyar da shi nayi ba, kuma shi abokin nawa ne ya kai ni wajen matar da ta bani bashin kudin, ina mata bayanin halin da nake ciki ta gamsu ta bani kudin.’ 

Copyright:
Leadership A yau


Post a Comment

 
Top