Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta musanta zargin da tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya yi mata cewa rashin adalcinta ne ya sa shi ficewa daga cikinta.
Malam Shekarau ya bar PDP ne ranar Talata da safe bayan ya zargi jam'iyyar da rusa shugabancinta na jiharsa sannan ta bai wa Sanata Rabi'u Kwankwaso -wanda bai dace da komawa cikinta ba - mukamai mafi tsoka a cikin kwamitin wucin gadin da ta nada a jihar.
Sai dai Malam Shehu Yusuf Kura, kakakin shugaban PDP na Najeriya, ya shaida wa AREWAR MU A YAU cewar tsohon gwamnan na Kano yana tattaunawa da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da zummar komawa APC.
"Tun sati takwas zuwa tara da suka gabata mun san yana magana da APC, mun san yana tattaunawa da gwamnan jihar Kano a kan mukamai da za a ba shi," in ji Shehu Yusuf Kura.
Sai dai TrustPosts ba ta tabbatar da wanan zargi nasa ba, kuma ya zuwa yanzu Malam Shekarau bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba.
Kakakin shugaban na PDP ya kara da cewa a shekarar 2014 lokacin da tsohon gwamnan na jihar Kano ya koma PDP daga APC an yi masa goma ta arziki inda aka mika masa jagorancin jam'iyyar duk da yake ya taras da wasu manyan 'yan siyasa a cikinta.
A cewar sa, bai kamata Malam Ibrahim Shekarau ya yi korafi ba don an ce za a bai wa bangaren Sanata Kwankwaso wasu mukamai a PDP "tun da ya shigo jam'iyyar tare da 'yan majalisa da tsohon mataimakin gwamna da sauran manyan 'yan siaysa."
Da ma dai masana harkokin siyasa na ganin Malam Shekaau da Sanata Kwankwaso ba za su taba zama a inuwa daya ba saboda tsananin sabanin siyasar da ke tsakani su.
Post a Comment
Post a Comment