An Yi Wa Wata Mata Yankan Rago A Jihar Katsina

Wani mara imani da har yanzu ba a san ko waye ba ya yi wa wata baiwar Allah mai suna Nana Maryam yankan rago tare da soka mata wuka.

An tsinci gawar wannan baiwar Allah ne a kauyen Gyarta da ke karamar hukumar Mashi da ke jihar Katsina a ranar Laraba da ta gabata  gawar dai an tsince ta ne a bayan gari, inda ake kyautata zaton cikin dare aka yanka ta.

Ita dai marigayiya Maryam bazawara ce da ake kokarin daura mata aure, wanda da a kwanannan ta gama idda.

Sai dai hukuma na nan na ta tsananta bincike tare da kokarin gano wanda ya aikata wannan mummunar ta'addanci.





Post a Comment

 
Top