Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hanni wajen tayar da hayaniya.

Jarumi mai tauraro Adam A.Zango ya gargadi yan uwanshi kan mayar da martani mai tayar da rigima kan wadanda ke zagin sa a shafukar sada zumunta.
Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hanni wajen tayar da hayaniya.
"DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA....ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA"ya rubuta.
Idan ba'a manta ba a kwanan baya jarumin da abokin aikin sa kuma kuma babban jigo na masana'antar kannywood Ali Nuhu sun samu sabani wanda ya tayar da iska tsakanin mabiyan su.

Ali Nuhu da Adam Zango sun sasanta
(instagram/Falalu_a_dorayi)
Duk da cewa jarumai sun sulhunta kansubayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki na masana'antar kannywood suka yi na neman kawo karshen rigimar dake tsakanin su wannan bai hana wasu daga cikin mabiyan sucigaba da yi ma juna kalaman batanci.
👉Duk masoyi na gari yayi musu fatan Alkhairi ta hanyar comment a kasa.
Post a Comment
Post a Comment