GYARA KAYAN KA: Matakan farko da zaka bi domin kiyaye shafin ka na Facebook daga masu kutse (Hackers)



Sakamakon wani bincike da muka gudanar akan mutanen da akeyiwa kutse a shafukansu na Facebook. Binciken ya yi nuni da kaso 80 bisa 100 na wadanda akayiwa kutse tare da sauya musu suna a shafin Facebook, anyi nasarar kutsawa cikin shafin su ne sakamakon sunyi amfani da lambar wayarsu a matsayin Password din Facebook dinsu.

Sanya lambar waya a matsayin Password din Facebook shi yake bawa masu kutse damar kutsawa cikin shafin Facebook dinka har su sauya maka sunanka. Masu kutsen dake kutsawa shafukan mutane a halim yanzu, ba wasu kwararru bane, kawai suna gwada amfani da abunda mutane suka yawaita sanyawa a matsayin Password dinsu ne.

Wasu sukan cire lambobi ukun farko daga cikin lambar wayarsu (080 ko 090 ko 070 ko 081) sai su sanya sauran a matsayin Password din su na Facebook, cire wadannan lambobi Ukun farko ba zai hana masu kutse kutsawa cikin shafinka ba.

Hanyar da zaka kare shafinka daga masu kutse shine: idan har kasan lambar wayar ka shine Password dinka, to ka hanzarta ka sauya password dinka don gudun kutsawar masu kutse cikin shafinka.


Post a Comment

 
Top